Mutane dari da casa'in da bakwai mutane ne da aka ga sunyi muamala da dan kasar Liberian nan da ya mutu da cutar a Najeria bayan ya sauka daga jirgin da ya shigo daga kasarsa akan hanyarsa ta zuwa Amurka.
Saboda mahimmanci da kuma dawainiyar cutar ne yasa tuni gwamnatin trayyar Najeriya ta kirawo taron majalisar ministoci da gwamnoni a Abuja domin hada kai a tabbatar an dauki matakai na bai daya domin a yaki bazuwar cutar.
Sai dai gwamnatin Najeriya tana alfahari da cewa a duk duniya babu wani dan Najeriya dake dauke da cutar in ba mutanen da suka yi muamala da dan kasan Liberia Patricl Sawyer wanda shi ne ya kawota Najeriya.
Gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Tanko Umar Al-makura ya kara yin bayani akan taron. Yace sun yi magana akan abubuwa da za'a yi musamman na yin rigakafi. A yiwa mutane gargadi da nasiha kada suyi sake ta yadda cutar zata addabesu. Kawo yanzu babu wani magani da zai iya warkar da ciwon. Kafin a samu magani duk wanda ya kamu da cutar za'a kebeshi ta yadda ba zai ba wani ba.
Taron dai bai shafi maganar siyasa ba. Taron akan maganar kiwon lafiya ne domin cutar ebola ta fi lahani da rigingimun siyasa. Cutar idan ta kama mutane to kashi casa'in cikin wadanda suka kamu da ita suna iya mutuwa. Abun da ya damu kasar kenan a wannan lokacin.
Gwamnonin jihohi zasu tabbatar da yin abubuwa uku. Na daya su tabbatar da rigakafi. Na biyu su kare ko kebe duk wadanda suka kamu da cutar domin kada su yadata cikin sauran mutane. Na uku za'a dauki matakan rage azabar cutar daga wadanda suka kamu da ita. Gwamnatoci zasu samar da kayan aiki da suka dace domin a gujewa kuskure wajen gano cutar.
Ga rahoton Umar Faruk Musa
Your browser doesn’t support HTML5