Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Karyata Batun Kamuwa da Cutar Ebola Sanadiyar Cin Kilishi


Ana gwada jinin mutane ko suna da cutar ebola
Ana gwada jinin mutane ko suna da cutar ebola

Tun daga ranar da Najeriya ta dauki matakan dakile yaduwar cutar ebola aka soma yiwa duk wadanda suke shiga kasar kwajin zafin jiki mai nasaba da cutar kafin a bari su shiga.

Ranar Litinin din nan an yiwa mutane kusan dari biyar gwaji a iyaka da jamhuriyar Benin kafin a bari su shigo kasar.

A filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja fiye da mutane dari tara suka shigo kasar kuma dukansu sai da aka yi masu gwaji. Ba'a samu kowa da zafin jikin da ya wuce kima ba.

Dr Nasiru Sani Gwarzo yayi karin bayani. Sai dai masu tsallakowa da kafa ba'a fara gwadasu ba har sai an kara yawan ma'aikata. Yace suna fatan nan da gobe za'a kara ma'aikata da zasu yi aiki akan iyakoki. Yace ban da haka a duk jihohi suna auna mutane.

Akan labarin da wasu suke rurutawa wai ana samun cutar ebola ta cin kilishi, Dr Gwarzo yace babu kashin gaskiya a batun. Ya kara da cewa ba'a samunsa a dabbobin gida sai na daji. Ko suma ba'a daukar cutar daga busashen nama sai danye ko wanda bai dahu ba sosai.

Akan mutanen da ake yiwa jinya wadanda suka kamu da cutar Dr Gwarzo yace saura mutane takwas kuma ana fatan zasu warware. Basu samo magani ba daga Amurka amma akwai magungunan karin jini da ruwan jiki da sauransu masu sa sauki. Ta yin hakan zasu mike domin daruruwa ma sun mike. Yace ba kowa ne ke mutuwa da ebola ba.

An ja kunnuwan masu shan ruwan gishiri domin idan suna da hawan jini to suna kara ma kansu wahala ne.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG