EFCC Ta Musanta Zargin Yi wa 'Yan Adawa Da Shugaba Buhari Bi Ta da Kulli

Sabon ginin EFCC a Abuja

Yayinda yake taro da masu ruwa da tsaki a Ibadan babban birnin jihar Oyo, shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya musanta zargin da wasu ke yi na cewa hukumar na yiwa masu adawa da gwamnatin Buhari bi ta da kulli ne kawai.

Shugaban hukumar hana zarmiya, cin hanci da rashawa ko EFCC a takaice, Ibrahim Magu, ya musanta cewa hukumar ta na yiwa masu adawa da shugaban Nigeria Muhammad Buhari bi ta da kulli.

Ibrahim Magu ya musanta hakan ne a wajen wani taron masu ruwa da tsaki a ofishin hukumar dake birnin Ibadan.

Taron ya samu halartar kungiyoyin farar hula da kungiyoyin addinai da kwararru. Ibrahim Magu ya ci gaba da cewa cin hanci shi ne abu daya da yake mayar da hannu agogo baya ga ci gaban Nigeria, musamman yadda yake shafar talakawa a karkara. A cewarsa saboda haka yaki da cin hanci da rashawa ba yaki ba ne kawai, ceton rayuwa ne. Magu yace, cin hanci ya yiwa kasar illa don haka dole ne a yakeshi.

Hukumar ta EFCC ta kai kararraki kotu fiye da 120 tsakanin watan Fabrairu zuwa watan Agustan wannan shekara.

Shiko shugaban kungiyar Shafa'udeen Islam, Farfesa Sabitu Olagoke, ya ce da tun farko kasar na da hukuma irin EFCC da an dade da ci gaba. Shi ko shugaban kungiyar Kiristocin Nigeria reshen jihar Oyo Pastor Benjamin Akanmu ya ce zasu ci gaba da ilmantar da jama'a akan illar cin hanci da rashawa. Ita ko shugabar hukumar wayar da kawunan jama'a a jihar Oyo Uwargida Dolapo Dosunmu, cewa ta yi "muna iya fara yaki da cin hanci da rashawa tun daga cikin al'umma na kasa har mu kaiga manya na sama"

A saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Hukumar EFCC Ya Musanta Zargin Yiwa 'Yan Adawa Bita-da-Kuli - 2' 14"