Shugaban ECOWAS ya ce ana bukatar a aikawa da sako mai karfi game da rikicin Mali

  • Ibrahim Garba

Shugaban juyin mulkin Mali Amadou Haya Sanogo kenan zagaye da wasu sojoji

Shugaban Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ya ce wajibi

Shugaban Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ya ce wajibi ne kungiyar ta aika da kwakkwaran sako ga sojojin tawayen da su ka kaddamar da juyin mulki a kasar Mali a makon jiya.

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya gaya wa wakilan kungiyar nan mai mambobin kasashe 15 cewa dole ne su dau mataki ba tare da bata lokaci ba don kare dimokaradiyya a Mali don ya zama darasi a fadin Afirka.

Mr. Ouattara ne Shugaban Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), wadda ta kira taron gaggawa a birnin Abidjan a yau Talata.

Kungiyar, wadda ke da tasiri kan tattalin arzikin Yammacin Afirka, na nazarin ko za ta dakatar da Mali daga zama mambanta ta kuma kakaba wasu karin takunkumai.

Amurka da kasashen Faranasa da Tarayyar Turai, tuni su ka dakatar da kai kayan agaji zuwa kasar Mali a matsayin martani.

Mataimakin Shugaban Kungiyar ta ECOWAS Toga Gayewea Mclntosh ya gaya wa Muryar Amurka cewa burin kungiyar shi ne tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali da dimokaradiyya.