Tawagar wakilan da shugabannin kasashen Afirka ta yamma suka tura ta janye shirin kai ziyara domin tattaunawa da shugabannin sojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali.
Hakan na faruwa ne bayan samun rahotannin cewa gungun masu goyon bayan juyin mulki na shirin gudanar da wata kazamar zanga-zanga nuna rashin amincewa da ziyarar tasu a babban filin jirgin saman da jami’an zasu sauka a birnin Bamako.
Wakilan shugabannin kasashen kungiyar bunkasa cinikayya da hadin kai da juna ta kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS)sun hada da shugabannin kasashen Ivory Coast, da Jumhuriyar Benin, da Nijer da kuma Burkina Faso, a yau Alhamis tun farko aka shirya zasu kai ziyara Bamako inda zasu tattauna da shugabannin sojin da suka gudanar da juyin mulki aga ko hakan zai taimaka aja hankalinsu su maida mulki hannun farar hular kasar Mali
Anji wani jami’in dake dake bada shawara ga shugaba Alassane Ouattara na Ivory Coast na cewa har jirgin saman dake dauke da shugaban kasa ya shiga sararin samaniyar kasar Mali, amma sai aka umarci matukan jirgin saman da su juya a koma gida saboda samun labarin shirin gudanar da zanga-zangar a filin jirgin saman Bamako.
ECOWAS ta shirya gudanar da taron gaggawa a birnin Abidjan domin nazartar halin da ake ciki.