Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan siyasar Mali sunyi Allah wadai da juyin mulki


Wasu sanannun ‘yan siyasar kasar Mali sunyi Allah wadai da juyin mulkin da soja suka yi na hambarar da gwamnatin shugaba Amadou Toumani Toure ana sauran makoni biyar ayi zaben shugaban kasa, zaben da ba zaiyi takara a cikinsa ba

Wasu sanannun ‘yan siyasar kasar Mali sunyi Allah wadai da juyin mulkin da soja suka yi na hambarar da gwamnatin shugaba Amadou Toumani Toure ana sauran makoni biyar ayi zaben shugaban kasa, zaben da ba zaiyi takara a cikinsa ba.

Jiya juma’a yan siyasar suka gabatar da sanarwa suna masu fadin cewa juyin mulkin koma baya ne sosai ga kasar ta Mali. Dan takarar shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita yana daga daga cikin wadanda suka bukaci a maida abubuwa kamar yadda suke ada ba tare da bata lokaci ba.

Tun da farko kungiyar kasashen Afrika tace shugaba Mali Amadou Toumani Toure yana nan lafiyarsa kalau a wani wuri da ba’a baiyana ba kusa da Bamako baban birnin kasar, kuma masu biyaya a gare shi ne suke kare shi.

Jiya juma’a shugaban juyin mulki Amadou Haya Sanago yace soja zasu sauka da za’ar an zabi sabon shugaban kasa ta hanyar democradiya, amma ya kara da cewa kila a dauki dan lokaci kafin aga wanzuwar haka. Yace ba za’a raunana shugaba Toure ba, amma kuma yaki ya baiyana inda shugaban yake.

Amirka da kungiyar kasashen turai suma sunyi Allah wadai da juyin mulkin, a yayinda kungiyar kasashen turai da bankin duniya suka dakatar da taimakon da suke baiwa kasar Mali. Ita kuma Amirka, a jiya juma’a tayi kashedi cewa, idan ba’a maido da mulki democradiya ba, to itama zata jingine taimakon da take baiwa kasar Mali.

XS
SM
MD
LG