Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tsinke Agaji Ga Gwamnatin Mali


Wani mutumi rike da kwalin da aka rubuta "A koma ga aiki da tsarin mulki" a jiki a lokacin zanga-zangar nuna kin jinin juyin mulkin da sojoji suka yi, Litinin 26 Maris 2012 a Bamako, babban birnin Mali.
Wani mutumi rike da kwalin da aka rubuta "A koma ga aiki da tsarin mulki" a jiki a lokacin zanga-zangar nuna kin jinin juyin mulkin da sojoji suka yi, Litinin 26 Maris 2012 a Bamako, babban birnin Mali.

Amma kuma hukumomi a Washington sun ce zasu ci gaba da bayar da agajin abinci da na jinkai ga kasar wadda sojoji suka kwace mulkinta

Amurka ta ce zata dakatar da agajin da take bayarwa ga gwamnatin kasar Mali, a bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a makon da ya shige.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Victoria Nuland, ta ce wannan shawara zata shafi agajin dala miliyan 60 zuwa 70. Amma ta ce Amurka zata ci gaba da bayar da agajin abinci da na jinkai ga kasar.

Ta ce sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta tattauna yau litinin da shugaba Alassane Ouattara na Cote D’Ivoire, ta kuma ce Amurka tana goyon bayan yunkurin da kungiyar ECOWAS keyi na warware lamarin na kasar Mali.

Tun farko a yau litinin, Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya fito da kakkausar harshe yana yin tur da kwace mulki da karfi da aka yi daga hannun gwamnatin kasar Mali wadda aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.

Kwamitin sulhun yayi kira ga sojoji da su koma cikin barikinsu, a maido da aiki da tsarin mulki, sannan a gudanar da zabe kamar yadda tun farko aka shirya yi a watan Afrilu.

Daruruwan mutane ma sun yi zanga-zangar nuna kin jinin wannan juyin mulki yau litinin a Bamako, babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG