Shugaban CAF Ahmed Ya Killace Kansa Bayan Ya Kamu Da Corona

Le président de la CAF, Ahmad Ahmad, lors d'une conférence de presse à Johannesburg, Afrique du Sud, le 7 avril 2017.

Hukumar kula da harkokin kwallon kafar Afirka, CAF, ta tabbatar da cewar shugaban hukumar Ahmad Ahmad ya kamu da cutar COVID-19.

Hukumar ta CAF ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar bayan an kwantar da shugaban nata a asibiti.

Ahmad, mai shekaru 60 da haifuwa ya nuna alamun cutar ne bayan ya dawo daga kasar Masar ranar Laraba 28 ga watan Oktoba, lamarin da ya sa aka gudanar da gwajin cutar a kansa kana aka tabbatar da ya harbu.

A halin yanzu Ahmad Ahmad, a ya killace kansa na akalla kwana 14 a hotel dinsa.

Shugaan CAF Ahmad Ahmad

Mutanen da suka yi mu’amala da shi cikin akalla kwanaki bakwai, musamman wadanda suke tare da shi a lokacin tafiyarsa zuwa kasar Morocco don kallon gasar cin kofin Confederation, su ma an bukaci su dauki matakan da suka dace.

Sai dai shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino wanda ya kamu da cutar wasu kwanaki ‘yan kadan da suka gabata, ya aike da sako ga Ahmad yana mai yi masa fatan samun sauki cikin gaggawa.

Shugaban FIFA Gianni Infantino

Shugaban hukumar CAF Ahmad Ahmad ya kuma kasance mataimakin shugaban hukumar FIFA.