Ahmad dan asalin kasar Madagsca wanda ya dauki ragamar shugabancin CAF a shekarar 2017, ya na samun goyon baya tun bai yanke shawarar sake shiga takarar zaben da za a yi a watan Maris 2021 ba.
Ranar 12 ga watan Nuwamba ce ranar karshe na shigar da takardun neman tsayawa takara ga duk mai neman yin takara.
Wata sanarwa da shugabannin yan-kunan Afrika shida suka sanyawa hannu, na nuni da cewa dan shekaru 60 na samun goyon baya ainun, idan ya yanke shawarar shiga takara, koda yake maganar shi ce a tsakiyar batun da hukumar FIFA ke yi.
A baya Ahmad ya ce sai ya nemi shwarar daga masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a nahiyar Afrika, kamun ya yanke shawarar shiga takara, yana mai cewa zai iya tsayawa saboda goyon bayan jama’a, amma ba dan bukatar kansa ba.
A watan da ya gabata, shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya Amaju Pinick, yaki janyewa daga neman shiga takara, inda yake cewa akwai abubuwa da dama da ba a yinsu dai-dai a hukumar ta CAF.
Facebook Forum