Mai yiwuwa a dage fafata gasar kwallon kafa ta cin kofin nahiyar Afirka ta shekara ta 2021, sakamakon yanayin da annobar coronavirus ta jefa kasashen duniya, ciki har da nahiyar Afirka.
A gobe Talata ne hukumar kwallon nahiyar Afirka ta CAF za ta gudanar da taro a karkashin jagorancin shugaban hukumar Ahmad Ahmad, domin tattauna al’amura da dama da suka shafi yadda za’a tunkari yanayin da ya yi sanadiyyar dakatar da lamurran kwallon kafa a nahiyar, ciki har da gasar ta cin kofin nahiyar Afirka da aka tsara gudanarwa a watannin Janairu da Fabrairun shekara mai zuwa ta 2021, tare da kasashen 24.
Mukaddashin babban sakataren hukumar ta CAF Abdelmounaim Bah, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP cewa, “mu na bukatar ci gaba da shirye-shiryen gudanar da gasar kamar yadda aka tsara tun farko, a watanni Janairu da Fabrairu masu zuwa.”
To sai dai kasashen Afirka da dama sun ji jiki sakamakon annobar ta coronavirus, kazalika ga kuma dokokin takaita zirga-zirga da tarukan jama’a, wanda ya sa kasashen da dama rurrufe kan iyakokinsu daga shigowar baki ‘yan kasashen waje.
Kasar Afirka ta kudu ce ta fi yawan cutar a nahiyar, inda alkaluma suka bayyana masu cutar ta COVID-19 a kasar 131,800, da kuma wadanda suka mutu sakamakon cutar 2,413.
Facebook Forum