KANO, NIGERIA - Wannan ziyara wani bangare ne na rangadin da ya fara a Afrika, inda ya gana da mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo da sauran Jami’an gwamnati.
Shugaban, wanda ya ziyarci biranen Abuja da Kano, ya sanya hannu a kan yajejeniyar hadin gwiwa ta samar da dala miliyan 500 domin aiwatar da wani sabon shirin bunkasa harkokin noma da dangoginsa a kasar.
A hira da wakilin Muryar Muryar, Dr Mansur Mukhtar, tsohon ministan harkokin kudi na Najeriya, kuma mataimakin shugaban bankin na Islamic Development Bank a yanzu, ya yi karin haske dangane da dalilan ziyarar da kuma abubuwan da suka tattauna da hukumomin kasar ta Najeriya.
Saurari cikakken rahoton da kuma yadda hirar tasu ta kaya da Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5