Shugaban Amurka Donald Trump, da Firai Ministan Japan, Shinzo Abe, za su yi wata ganawa kafin babban taron da aka tsara za a yi tsakanin Trump da shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong Un, a cewar jami’an kasar ta Japan.
Shugaba Trump ya tattauna da Abe a jiya Litinin, yayin da jami’an Amurka suka je Korea ta Arewa da Singapore, domin tsara yadda tattaunawar za ta gudana.
Sai dai Fadar gwamnati ta White House ba ta amsa tambayoyin da Muryar Amurka ta yi mata ba, kan ganawar ta Trump da Abe.
Kusan Amurkawa dubu 34 suka mutu a yankin Korea, sanadiyar ta-da jijiyar wuyar da aka kwashe shekaru uku ana yi a yankin.
A shekarar alif-dari-tara-da-hamsin-da-uku ne hankula suka kwanta a yankin, sanadiyar wani shirin tsagaita wuta da aka cimma, amma ba tare da an rattaba hannu akan wata yarjejeniyar zaman lafiya ba.
Trump da Abe dai za su halarci wani taron koli na tattalin arziki da za a yi na kasashe bakwai da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, wanda za a yi Canada.
Jami’an Amurka da na Korea ta Arewa sun hadu a yankin Korea, wanda baya dauke da sojoji a ranar Litinin.