Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Korea ta Arewa Na Kokarin Farfado Da Tattaunawarsu


Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Korea ta Arewa Kim Jung Un
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Korea ta Arewa Kim Jung Un

Kwana daya bayan da ya soke tattaunawa da shugaban Korea ta Arewa shugaban Amurka Donald Trump ya aika da wata tawagar farfado da shirin taron kolin domin shugabanninsu gana a wata mai zuwa.

Jami'an Amurka da na Korea ta Arewa sun gana a jiya Lahadi a tsibirin nan da aka cire jami’an soji, domin su tattauna yiwuwar ganawa tsakanin shugaba Donald Trump da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa Kim Jong Un.

Bayan dakatar da tattaunawar a ranar Alhamis din nan da ta gabata Shugaba Trump ya ce ba shakka ganawar za ta iya yiwuwa a ranar 12 ga watan gobe kamar yadda aka tsara a kasar Singapore.

“Za mu yi nasara a yunkurin kwance damarar makamin nikiliyan a zirin Korea, wanda haka wani babban abu ne ga kasar ta Korea ta Arewa, haka ma wannan wani babban abu ne ga Korea ta Kudu, da Japan,da ma duniya baki daya, dama Amurka." Inji Trump.

Sai dai abinda aka kasa ganewa shi ne yadda Trump cikin dan kankanin lokaci ya sauya ra’ayinsa akan son ya gana da Kim, kwana daya bayan ya jingine maganar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG