Shugaban Amurka Joe Biden Ya Shiga Kakar Hutun Shi Na Karshe A Fadar White-House

Shugaban Amurka Joe Biden yayin afuwa ga Talotalo a fadar white House

Shugaban Amurka Joe Biden ya shiga kakar hutun shi na karshe a fadar House, tare da yin abinda aka saba bisa al’ada na mika Talotalo guda biyu da za’a yi amfani dasu a teburin  bikin ranar nuna godiya na ‘Thanks giving’ a turance a kudancin Minnesota.

Biden ya marabci baki 2,500 a farfajiyar filin da ya kasance karkashin hasken rana, inda ya rika jefa barkwanci cikin annashuwa game da kyawawan launukan dake wurin, da magana kan makonnin karshe na shugabancin shi, bayan shafe kusan rabin karni yana zagayawa kan madafan iko a Washington.

Biden mai shekaru 82 yanzu a duniya, yace, hakan ya kasance abin alfahari a rayuwar sa, da kasancewa mai godiya har abada, bisa la’akari da ganin zuwa ranar 20 ga watan Janairu mai zuwa ne zai sauka daga kujerar shugabancin kasar.

Daganan har zuwa ranar da za’a kaddamar da sabon shugaban kasa, shugaba Biden da maidakin shi Jill Biden zasu cigaba da kasancewa cikin hidindimu iri dabam dabam, da zasu hada dana yin bankwana. Jadawalin aiyuka a fadar white House a watan Disamba zasu cika ne da bukukuwan ranakun hutu iri dabam dabam. Daga ma’aikatan bangaren da ake cema ‘west wing’ da yan majalisa da ayarin yan jarida na fadar white House.

Biden ya hada hancin bikin ne dayin sakin Talotalon da sunan fulawar a hukumance ta gidan shugaban kasar da ke Delaware.

A nata bangaren, a ranar Litinin dinne uwargidan Shugaban kasar Jill Biden ta karbi iccen kirsimeti a hukumance a fadar white House da za’a yi ado da shi a wurin da ake kira ‘Blue Room’. Itacen mai tsawon kafa 18.5 (mita 5.64) na’ Frasser Fir’ ya zo ne daga wata gona dake yankin Arewacin North Carolina, a kwanannan ya gamu da iftila’in mahaukaciyar iska mai tafe da mamakon ruwan sama da akaima lakabi da Hurricane Helene.