Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Tana Shirin Tattauawa Da Manyan Kashen Turai 3 Akan Shirin Ta Na Nikiliya


Iran's head of the Atomic Energy Organisation Mohammad Eslami (R) and the United Nations nuclear chief Rafael Grossi give a joint press conference in Tehran on November 14, 2024.
Iran's head of the Atomic Energy Organisation Mohammad Eslami (R) and the United Nations nuclear chief Rafael Grossi give a joint press conference in Tehran on November 14, 2024.

Kyodo ta ce gwamnatin shugaban Iran Masoud Pezekshkian tana neman mafita akan wannan batu da aka kasa cimma matsaya a kai kafin sabon shugaban Amurka Donald Trump ya sha rantusuwar kama aiko a watan Janairu

Kafar watsa labaran Japan Kyodo ta bada rahoto yau lahadi cewa, Iran tana Shirin tattaunawa da wasu manyan kasahen Turai 3 akan Shirin ta na Nukiliya wanda za ayi a ranar 29 a Geneva, 'yan kwanaki bayan da hukumar MDD dake bibiyar al’amuran makamashi ta cimma matsayar kin amincewa da shirin Tehran.

Iran ta mai da martini kan matsayar, wanda Birtaniya, Faransa,Jamus da Amurka suka gabatar, lamarin da jami’an gwamnati suka ayyana da matakai mabanbanta da suka hada da farfado da wasu sabbin na’urori da zasu taimaka wajen samar da sinadarin Uranium.

Mai Magana da yawun ma’aikatar wajen Iran ya ce kasar zata tattauna da Birtaniya, Faransa da Jamus a ranar Jumma’a, inda aka yi amanna cewa kasashen suna neman sake farfado da wata yarjejeniyyar samar da nukiliya da aka kasa cimmawa a 2015.

A wa’adin mulkin shi na farko a 2018, Trump ya janye daga yarjejeniyar. A matsayin martanin matakin na Amurka, Iran ta zarta ka'idar da aka bata na yawan nukiliyan da yarjejeniyyar ta amince ta samar.

Tattaunawar da ake shirin yi tsakann Iran da manyan kasashen Turan 3 da tarayyar Turai zata kasance mai sasantawa, zai kasance tattaunawar farko da kasar zata yi tun bayan da sabon shugaban kasar mai ra’ayin gyara Masoud Pezekshkian wanda ya gaji tsohon shugaban kasar Ebrahim Raisi wanda ya mutu a wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan Mayu ya kama aiki a karshen watan Yuli.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG