Shugaban Amurka Barack Obama ya kammala balaguronsa

Shugaban Amurka Barack Obama

A daren Litinin din jiya ne Shugaban Amurka Barack Obama ya dawo birnin Washington DC daga doguwar tafiyar da yayi, wacce ta kai shi kasashen Saudiyya, Birtaniya da Jamus. A lokacin wannan tafiya Obama ya jaddada amfanin kawancen Amurka.

Musamman game da yadda yake kallon hakan a matsayin abin bukatar yi domin dakile ‘yan ta’addar ISIS, tare da ganin an wargaza shirin Rasha a Ukraine da Syria. A ziyarar shugaban ta kasashen ketare.

A lokacin wannan tafiya zuwa kasashen ketare a kokarinsa na saita akalar abubuwan da ya yi don ‘yan baya, Obama yayi kira a wani jawabin da yayi a Jamus a jiya Litinin cewa, Turai na fuskantan mawuyacin hali.

To amma ya kamata shugabanin yankin su saka idanu wajen rashin daidaiton kudaden shiga da ilimin matasa, da daidaita albashin mata. Shugaban yace, idan har bamu magance wadannan matsaloli ba, to bata gari zasu yi amfani da wannan dama.

Wajen karkata akalar matsalolin ta hanyar amfani da abinda ake fargaba zuwa hanyoyin rusa al’umma.