Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da wasu kasashe sun bukaci a kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Amurka da China da wasu manyan kasashen duniya sun bukaci a kawo karshen rikicin dake hana ruwa gudu a shirin samun masalaha tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawayen kasar.

Jiya Alhamis kasashe goma da kasashen tarayyar Turai da kungiyar kasashen Afirka suka bada wa'adi inda suka suna sa ran madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar zai tattara nashi i nashi ya koma Juba babban birnin kasar tsakanin jiya da gobe Afirilu 23.

Kungiyoyin kasashen sun yi masa kashedi cewa idan ya yi kunnen shegu da wa'adin da suka bashi zasu gabatar da maganar gaban Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin tsaro na kungiyar kasashen Afirka. Ba zasu tsaya nan ba. Zasu bukaci a dauki mataki.

Yakamata Riek Machar a ce ya koma Juba wannan makon domin a sake rantsar dashi mataimakin shugaban kasa da zummar kafa gwamnatin wucin gadi. Sai dai bai tafi Juba ba ranar Litinin da kuma Talata saboda rashin cimma jituwa akan adadin sojojinsa da zasu mara masa baya da makaman da zai iya shiga dasu birnin.

Ana ganin komawar Machar zata yi tasiri kan cigaba da shirin zaman lafiya da bangarorin biyu suka rabtawa hannu watan Agustan bara domin kawo karshen rikicin kasar da yanzu ya shiga shekaru biyu da rabi, rikicin da kuma ya raba kimanin mutane miliyan biyu da dubu dari da muhallansu

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG