Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Obama zai kara tura sojoji zuwa Syria


Shugaba Obama na Amurka da shugabar kasar Jamus Angela Merkel
Shugaba Obama na Amurka da shugabar kasar Jamus Angela Merkel

Shugaban Amurka Barack Obama na shirin kara tura sojoji 250 zuwa Syria dominb su taimaki 'yan hamayya dake fafatawa da kungiyar ISIS kamar yadda wasu jami'an gwamnatin Obama suka sanar jiya Lahadi

Shugaban zai bayyana wannan sabon shirin ne a wata sanarwa da zai yi yau Litinin a Hanover dake kasar Jamus inda yanzu yake ziyara.

Ziyarar kasar Jamus ita ce ta karshe a jerin kasashe uku da ya kai ziyarar mako daya da suka hada da Jamus, Birtaniya da Saudiya. A kasashen shugaban ya tattauna da takwarorinsa akan barazanar da kungiyar ISIS take yiwa duniya.

Karin sojojin da za'a tura zuwa Syria zasu hada da likitoci da jami'an leken asiri. Karin zai sa adadin sojojin Amurka a Syria su kai 300.

Tun farko Shugaba Obama ya fada ta kafar talibijan din BBCcewa kokarin kawo karshen rikicin Syria ba zai kasance na yin anfani da karfin soji ba ne kadai.

Yace maimakon kutsawa kasar Syria da karfin soji kamata ya yi kasashen duniya su matsawa Rasha da Iran lamba domin su ne suke marawa shugaban Syria Bashir al-Assad baya. Idan a matsawa kasashen biyu ana iya cimma yarjejeniyar zaman lafiya tare da kafa gwamnatin wucin gadi.

Yayinda shugaban yace ba za'a mamaye Syria ba amma hare haren jiragen sama da Amurka ke jagoranta zasu cigaba musamman akan kungiyar ISIS a wurare kamar Raqqa da Mosul da zummar toshe hanyoyin da kungiyar ke anfani dasu tana aikawa da 'yan ta'ada zuwa nahiyar Turai.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG