Shugaban Amurka Barack Obama Ya Kai Ziyara Mai Tarihi Kasar Vietnam

Shugaban Amurka Barack Obama yayinda yake saukowa daga jirginsa a Hanoi babban birnin kasar Vietnam jiya Lahadi

Amurka da Vietman sun kwashe shekara da shekaru suna yaki tsakaninsu, mummunan yakin da ya lakume rayuka da dama daga bangarorin biyu

Shekaru arba'in da daya da yaki tsakanin Amurka da Vietnam ya kawo karshe ke nan, yakin da ya fi raba kawunan amurkawa a tarihin kasar, yanzu akwai dangantaka kwakwara tsakaninsu.

Bugu da kari akwai 'yan kasashen biyu, musamman a ma'akatun harkokin tsaron kasashen da suke cewa yakamata gwamnatin Shugaba Obama ta kara karfafa danganta tsakanin kasashen biyu ta cirewa kasar Vietman takunkumin hana sayar mata kayan yaki.

Shugaba Obama yana da ikon cire takunkumin ba tare da neman goyon bayan majalisun kasar ba to saidai wani a gwamnatin Amurka na ganin shugaban ba zai yi haka ba. Zai gwammace ya samu goyon bayan kwamitin tsaro na majalisar dattawa wanda Sanata John McCain na jam'iyyar Republican ke jagoranta. Sanata din ya ga yadda aka samu canji a kasar ta Vietnam amma kada amanta yana soji lokacin yakin.

Sanata McCain wanda ya sha kaye a hannu Obama a zaben shekarar 2008 sojan mayakin ruwa ne matukin jirgin yakin sama amma mai sauka kan ruwa. Lokacin yakin sojojin Vietnam sun harbo jirginsa suka cafkeshi har ya yi zaman kurkuku mai tsanin gaske inda suka gana masa muguwar azaba har ta tsawon shekaru biyar da rabi kafin Allah ya kubutar dashi.

To saidai duk da ukubar da ya sha, Sanata McCain ya yafe ,bai rike kowa a zuciyarsa ba. Ya amince da sasantawa tsakanin kasashen biyu kuma yace akwai wasu da suka gana masa azaba yana kuma fatan ba zai sake ganinsu ba.. Yace duk da haka mutanen Vietnam mutanen kwarai ne kuma abokan gaskiya ne. Yace kasashen biyu na bukatar juna. Yana ganin haske a dangantakar kasashen nan gaba tare da begen alamura zasu gyaru ainun.

Sanata John McCain tsohon soja wanda sojojin vietnam suka cafke suka kuma tsareshi har na tsawon shekaru biyar da rabi