Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Ta Amince Ta Bada Kudin Yakar Cutar Zika


Shugabannin Majalisar Dattawan Amurka suna jawabi akan cutar zika
Shugabannin Majalisar Dattawan Amurka suna jawabi akan cutar zika

Bayan sun sha kai da komo 'yan majalisar dattawan Amurka sun amince da ba gwamnati kudaden da suka kusa kai yawan adadin da ta nema domin ta yaki cutar zika

Majalaisar dattijan Amurka ta amince da kasafin kudi dala miliyan dubu daya da miliyan dari domin a yaki cutar Zika, kasa da abunda gwamnatin shugaba Obama ta nema, amma kuma ya ninka abunda majalisar wakilai ta kasafta.

Jiya Talata, majalisar da jam'iyyar Republican take da rinjaye ta amince da kasafin da kuri'u 68-29 bayan da majalisar tunda farko taki ta amince da duka abun da gwamnatin ta nema,wace ta gabatar cikin watan Febrairu, sakamkon gargadin da kwararu ta fuskar kiwon lafiya suka yi cewa cutar tana iya bazuwa a sassan Amurka mai yawa.

Cutar da sauro ke yadawa tana iya haddasa mummunar nakasa ga jarirai, wacce aka danganta da matsaloli da suka jibanci kwakwalwa.

Ire-iren sauron dake haddasa cutar zika mai gurbata kwakwalwar jariri ta hana girma
Ire-iren sauron dake haddasa cutar zika mai gurbata kwakwalwar jariri ta hana girma

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG