A Yau Laraba ne ake kyatata zaton Shugaba Donald Trump zai gana da shugabannin majalisun tarayyar da ya gayyata zuwa fadar White House a domin ganawa akan harkar tsaron kan iyakar kasar, yayin da wasu ma’aikatun gwmanati su ke a rufe.
Shugaban ya fada a jiya talata cewa, a shirye ya ke daya amince da tattaunawar da zata kawo karshen rufe wasu ma’aikatun gwamnati wanda ya shiga rana ta goma sha daya a sabuwar shekara da muka shiga a jiya daya ga watan Janairu, amma ya dage da cewa duk yarjejeniyar da za a kulla dole ta hada da kudin da za’a gina katanga mai kyau a tsakanin iyakar Amurka da Mexico.
Yanzu haka bayan kwana goma sha daya babu wani ci gaba, shugaban ya nuna alamu cewa a shirye yake ya amince da yarjejeniya a wani sako daya aika ta shafinsa na Twitter.
A ranar Alhamis mai zuwa ne sabuwar majalisar wakilai zata bude, kuma ana kyautata zaton shugabannin ‘yan jam’iyyar Democrat za su gaggauta amincewa da wata doka da zata bada damar sake bude ma’aikatun gwamnati, da dawo da sama da ma’aikatan gwamnatin tarayya 800,000 kan aikin su da kuma biyan su akan lokaci. Sai dai kudaden da ‘yan majalisar na Democrat za su amince da su a cikin dokar, ba za su hada har da kudaden da shugaba Trunp ke nema na gina Katanga a kudancin iyakar Amurka da Mexico ba. Ko da yake babu tabbacin cewa majalisar dattawa za ta amince da dokar.