Yau Litini an shiga rana ta 10 a jere da rufe wasu ma'aikatun gwamnatin tarayyar Amurka, kuma har yanzu babu wata alamar yiwuwar sasantawa, yayin da har yanzu tattaunawa tsakanin Shugaba Donald Trump da 'yan majalisar dokokin tarayyar Amurka ke cigaba da cijewa.
Shugaba Trump na cigaba da bukatar biliyoyin daloli domin gina Katanga tsakanin iyakar Amurka da Mexico. ‘Yan jam'iyyar Demokarat a majalisar dokokin tarayyar Amurka na goyon bayan karin kudi kadan ne saboda tsaron kan iyaka , amma sun ki yarda da batun gina katangar. Wa'adin kasafin kudin rubu'i daya na gwamnatin tarayyar Amurka ya cika tun ranar 22 ga watannan na Disamba.
Jami’an fadar shugaban Amurka ta White House sun zauna domin cimma matsaya amma hakan bata samu ba.
A ranar lahadi shugaba Trump ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, ‘yan jam’iyyar Democrate sun bar gari, kuma basu damu da lafiya da kuma harkar tsaron Amurkawa ba.
Facebook Forum