Shugaban Amurka Donald Trump ya maida martani da kakkausan lafazi jiya litinin akan samamen da hukumar binciken Amurka ta FBI ta kaiwa ofishin lauyan sa, Michael Cohen, yana mai kiran wannan matakin “abin kunya, kuma wani “sabon salon rashin kyautatawa”.
Hukumar ta FBI ta sami sammacin binciken ofishi da kuma otel din da Cohen ya ke zama don kwace wasu takardun kudi da kuma wasu takardun bayanai, ciki har da wadanda suka danganci biyan kudi dala 130,000 na rufar baki da Cohen ya ba wata ‘yar wasan fina-finan batsa mai suna Stormy Daniels.
Masu masaniyi akan batun sun fadawa jaridar Washington Post da ta New York Times cewa ana binciken Cohen akan yiwuwar wata badakalar kudadenn banki.
Babban lauyan Cohen, Stephen Ryan, ya fadi cewa binciken na zaman wani bangaren bukatar da mai bincike na musamman Robert Muller ya gabatar, Muller dai ya kwashe shekara daya yana binciken yiwuwar katsalandan Rasha a zaben shugaban kasa na Amurka da aka yi a shekarar 2016, da kuma yiwuwar alakar wadanda suka yiwa Trump yakin neman zabe da Rashar.