Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Samamen FBI a Ofishin Lauyansa Abin Kunya Ne


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

Samamen da FBI ta kai kan ofishin lauyan shugaban Amurka Donald Trump ya sa shugaban cewa samamen tamkar yaki ne akan kasar Amurka kuma abun kunya ne

A wata sabuwa kuma, shugaba Donald Trump ya kira samamen da aka kai kan ofishin lauyansa Micheal Cohen a zaman "abin kunya," yace wannan hari ne akan kasarmu kuma wani "sabon babi sukutum na rashin adalci."

Da aka tambayeshi mai yasa bai zai kori mai bincike na musamman kan zargin hadin bakin kwamitin kempensa da Rasha Robert Mueller ba, Trump yace zamu ga abin da zai faru. Yace ina gani wannan wani abin kunya ne kuma mutane da dama suna ganin haka. Wannan wani bita da kulli ne a fili.


Trump ya kara da cewa, a lokacin da ya kori tsohon shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta FBI Jmaes Comey, "abunda ya tabbata shine matakin da na dauka yayi dai dai."


Jaridar Washington Post ta fada jiya Litinin da maraice cewa, anabincike a kan Cohen ne kan yiwuwar zambatar banki, ha'inci, da kuma karya dokokin amfani da kudaden yakin neman zabe,a cewar wani dake da masaniya a kan batun.

Hukumar FBI ta kai samame ne a jiya Litinin a ofishin Cohen kuma ta kwace wasu takardu, ciki har da masu alaka da batun lalata da Trump ya yi da wata mashahuriyar mai wasan fina finan batsa.


Jaridar New York Times ce ta fara bada labarin samamen da FBI ta kaiwa lauyan shugaba Trump.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG