Shugaban Amurkas Donald Trump ya isa Beijing yau laraba, ziyararsa ta farko a matsayin shugaban Amurka, kasar da ya sakawa ido, galibi da kallo maras kyau,a yunkurinsa na samar da ayyukan yi anan Amurka.Batun cinikayya shine jigo akan ajendarsa, da kuma batun Koriya ta Arewa.
Jami'an fadar white House suka ce shugaban na Amurka yana da niyyar matsawa China lamba, kawar Koriya ta Arewa, kuma babbar abokiyar cinikayyar Chinan, ta hurawa Koriya ta arewar wuta, ta yi watsi da shirin Nukiliyarta, wanda shine jigo a jawabi da ya gabatar a majalisar dokokin Koriya ta kudu sa'o'i kamin ya tashi zuwa China.
A jawabin shugaba Trump, yayi kira da kakkausar lafazi ga shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya kakkabe hannayensa kan mallakar makaman Nukiliya, domin ya sami damar "hawa kan siradi mai kyau."
Mr. Trump ya gargadi Koriya ta Arewa "kada ta gwada ko ta rena matsayar mu. Zamu kare tsaron mu da ci gaban mu da 'yancin walwalar mu."