Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Talata Shugaban Amurka Donald Trump Ya Isa Koriya ta Kudu


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Koriya ta Kudu, kasar dake makwaftaka da Koriya ta Arewa wadda take takaddama da Amurka akan shirinta na mallakar makaman nukiliya tare da yiwa Amurka barazanar kai mata hari

A yau Talata shugaban Amurka Donald Trump ya isa kasar Koriya ta Kudu, a zaman wani bangare na ziyara da yake yi a yankin wanda batun shirin makaman Koriya ta Arewa ya mamaye ta.

A yayin wannan ziyara ta kwanaki biyu, ana sa ran Trump zai tabbatar da kudurin Amurka na kare kawayenta daga barazanar Koriya ta Arewa, a yayinda ake fama da karin zaman ‘dar ‘dara zirin Koriyar.

A farkon makon nan a Japan, Trump da Prime Ministan Japan Shinzo Abe, suka amince da cewa har yanzu akwai sauran zabin da za’a iya amfanin da su, idan aka zo batun Koriya ta Arewa.

A cewar Shinzo Abe jiya Litinin, a wani taron manema labarai da yayi da Trump, yace, “babu wani amfanin zaman tattaunawa da Koriya ta Arewa” kuma lokaci yayi da ya kamata a matsawa Pyongyang lamba sosai.

Bayan tarurrukan da suka yi a ranar ta biyu, Abe da Trump, sun tabbatar da cewa batun Koriya ta Arewa ya kanainaiye tattaunawarsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG