Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Sami Bayanan Sirri Kan Rikicin Nukiliyar Da Koriya Ta Arewa.


Shugaba Trump Da Uwargidansa Melania, da furannin Hawa'ii da aka karrama su da su.
Shugaba Trump Da Uwargidansa Melania, da furannin Hawa'ii da aka karrama su da su.

Ranar Jumma'a shugaban ya sauka a Hawa'ii inda daga nan ne zai tashi zuwa Asiya.

A dai dai lokacinda zaman dar dar ta karu a makuridn koriya, rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Pacific a jiya jumma'a, ya gabatar wa shugaban Amurka Donald Trump bayanan sirri.

Rundunar ta gabatar da wannan bayanan ne da saukar jirgin shugaban na Amurka da ake kira "Air Force One" da turanci, a tsibirin Oahu, ind a shi da uwargidansa Melania Trump suka sami tarbo ta gargajiyar Hawa'II inda aka saka musu makawiyar furanni da ake kira Leis.

Daga nan shugaba Trump ya wuce kai tsaye zuwa cibiyar rundunar sojojin kundunbalar Amurka mai kula da yankin Pacific, runduna mafi girma wacce ta hada duka sassan mayakan Amurka.

"Kuna da jarumai da dakaru masu basira, kuma muna farin ciki da godiya," shugaba Trump ya gayawa Admiral Harry Harris, wanda shine kwamandan rundunar ta yankin Pacific.

Bayan da aka yiwa shugaban bayani, sai shida uwargidansa suka ajiye furanni a baraguzan jirgin yaki na ruwan Amurka mai suna USS Arizona wadda ya nutse ranar 7 ga watan Disemba shekara ta 1941, bayan harin da Japan ta kai a tashar jiragen ruwan Amurka dake Pearl Harbor, mataki da ya tusnduma Amurka a yakin duniya na biyu.

Kamin ya isa Phillipines, shugaban na Amurka zai yada zango a Japan,da KTK, da China da Vietnam, balaguro mafi tsawo da zai yi tun bayan da ya zama shugaban Amurka.

A lokacin ziyarar shugaban zai halarci taron kungiyar kasashe dake gabashin Asia, da na kasashe dake kungiyar kasashe dake kudu maso gabashin Asia da ake kira (ASEAN) a takaice.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG