Shugaba Trump Na Kara Neman Tsaurara Matakai Akan Bakin Haure

Donald J. Trump

Ta yiwu shugaban Amurka ya kara tsaurara matakai akan neman mafaka a Amurka, a yayinda yake ci gaba da nuna cewa 'Yan Jam'iyyar Democrat 'yan hana ruwa gudu ne.

Shugaban Amurka Donald Trump na kara kawo wata sabuwar fargabar al’umma akan batun bakin haure a yayinda ya rage saura ‘yan kwanaki kafin a yi zaben ‘yan majalisar dokokin Amurka mako mai zuwa, kuma ta yiwu shugaban ya kara tsaurara matakai akan bakin dake neman mafaka a Amurka yau Alhamis.

Shugaban na Amurka yayi magana akan baki a fadarsa ta White House, daya daga cikin matakan da yake dauka a baya-bayan nan na maida batun ya zama mai muhimmanci ga ‘yan jam’iyyar Republican a zaben da za a yi ranar Talata mai zuwa. Daga nan kuma zai je gangamin yakin neman zabe a jihar Missouri dake yankin yammacin-tsakiyar Amurka.

A wata sabuwar tallar yakin neman zabe da ya sanya a shafinsa na twitter jiya Laraba, Trump ya fada, amma ba tareda gabatar da wata hujja ba, cewa, ‘yan jam’iyyar Democrats sun bar wani mutum dan kasar Mexico mai suna Luis Bracamontes da aka maida kasarsa har sau biyu ya zauna Amurka inda kuma ya kashe wasu jami’an ‘yan sanda biyu a jihar California a shekarar 2014.