Trump yace rukunin mutane ne masu hadari,yayinda yake magana a kan bakin hauren, wadanda da farko ya kira "miyagun mutane da kuma 'yan kungiyar daba"
Wata mata da ta fito daga kasar El Salvador kuma take cikin tawagar bakin hauren da suka taso daga Arewacin Amurka, tace tana son Trump ya sani cewa ita da sauran mutane ba masu aikata laifi bane.
Tace “bawai zamu je can bane domin muyi sata ko mu cutar da wani bane. Muna son muyi aiki da hannayenmu da gumunmu domin mu samu abin kanmu. Muna rokon Allah ya kaimu can mu samu aiki.”
Sojoji dubu 15 da Trump yace zai aika, sun wuce yawan sojoijn da ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta sanar cewa tana shirin aiki dakaru 5,200 domin haduwa da dogarawan tsaron kasa 2,100 da yanzu haka suke bakin iyaka. Jami’an ma’aikatar tsaron Amurka sun fadawa Muryar Amurka cewa kusan sojoji 2,000 za a saka cikin shirin ko ta kwana, domin su taimakawa sojojin da aka riga aka tura bakin iyakar.
Wanda hakan ke nuna yawan sojojin da aka tura bakin iyakar Amurka sun wuce na sojojin Amurka dake yakar kungiyoyin ta’adda a Iraqi da Syria.
Facebook Forum