Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jajanta wa iyalan wadanda wata mummunar gobara ta rutsa da su sakamakon hadarin da wata motar dakon man fetur ta yi a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers, kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mai ba shugaban kasa shawara a fannin yada labarai ta bayyana.
Da yake jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Rivers kan mummunan lamarin, wanda ya yi sanadin hasarar rayuka da dukiyoyin jama’a, shugaba Tinubu ya yi wa wadanda suka jikkata addu’ar Allah ya basu lafiya.
Shugaban ya kuma umurci hukumomin tarayya a jihar da su samar da tallafin da ake bukata ga duk wadanda lamarin ya shafa.
A yammacin ranar Juma’a ne dai wata babbar tankar mai ta kara da wata motar, lamarin da ya sa mai malala har gobara ta tashi. Motoci 70 ne suka kone kurmus, a cewar rundunar ‘yan sandan jihar Rivers.
Jami’ar ‘yan sandan jihar Rivers DSP Grace Iringe-Koko, ta ce akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu sakamakon hadarin wasu da yawa kuma suka jikkata, wadanda tuni aka garzaya da su asibitoci dabam dabam a birnin Fatakwal.
Saurari rahoton Lamido Abubakar Sokoto:
Your browser doesn’t support HTML5