Shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe ya soke ziyarar aikin day a shirya kaiwa kasar Switzerland domin halartar taron kasa da kasa da MDD ta shirya yi a can. Hakan ta faru ne bayan da Switzerland ta hana baiwa uwargidansa da jami’anta iznin shiga kasa wato (Biza).
Kafofin labarai a Zimbabwe sun bata labarin cewa jami’an jakadancin kasa da kasa sun nuna takaicion wannan matakain hana Bizar da Switzerland ta dauka na hana biza. Jami’an Jakadancin kasa da kasa sun kuma soki lamirin kasar Switzerland suka ce hakan ya sabawa ka’idojin zumuncin da MDD ta shimfida. Ofishin jakadancin kasar Switzerland yaki cewa uffan game da wannan zargi.
Kasashen Amurka da Tarayyar Turaia sun azawa Zimbabwe takunkumin hana zirga-zirga a kan shugaba Mugabe da mafi yawan jami’an dake yiwa Gwamnatinsa hidima.