An gudanar da wata zanga-zangar nuna kin amincewa da rashin aikin yi a Afirka ta kudu. Mutane sama da dubu biyu ne suka shiga zanga-zanga a birnin Johannesburg. Masu zanga-zangar na bukatar ganin Gwamnatin Afirka ta kudu ta karfafa daukan matakin rage aikin yi a kasa da kuma fatarar dake addabar jama’a.
Shugaban kungiyar matasan jam’iyyar ANC, Julius Mlema ne yayi jagorancin shirya zanga-zangar. An dai san yadda Malema ke karfafa dagewar ganin sai Gwamnatin Afirka ta kudu ta kwace dukkan baraman tagulla da Azurfar su koma karkashin Gwamnatin Afirka ta kudu maimakon karkashin n’yan kasuwa. Anga masu zanga-zangar na wake-wake da rawa a kan tituna suna kuma nuna damuwar ganin yadda rashin aikin yi ka karuwa a tsakanin matasan Afirka ta kudu. Masu zanga-zangar sun yi kukan cewa yanzu yawan maras aikin yi a Afirka ta kudu ya daga zuwa kashi 25 daga cikin dari. Anga wata rundunar ‘yan sandan Afirka ta kudu na tsaye domin nazartar yadda ake gudanar da zanga-zangar ta ranar Alhamis.
A kalla mutane 2,000 ne suka yi zanga-zanga ran Alhamis a Afirka ta kudu kan rashin ayyukan yi a kasar
An gudanar da wata zanga-zangar nuna kin amincewa da rashin aikin yi a Afirka ta kudu. Mutane sama da dubu biyu ne suka shiga zanga-zanga a birnin Johannesburg.