Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Islama Ta Lashe Zaben Tunisiya


Wata mai goyon bayan jam'iyyar Ennahdha dauke da tutar kasar Tunisiya lokacin wani gangamin siyasa a Ben Arous, wanda ke kudu da birnin Tunis, October 21, 2011.
Wata mai goyon bayan jam'iyyar Ennahdha dauke da tutar kasar Tunisiya lokacin wani gangamin siyasa a Ben Arous, wanda ke kudu da birnin Tunis, October 21, 2011.

Kiyasin farko ya nuna cewa jam'iyyar Ennahdha zata samu akalla kashi 40 cikin 100 na kuri;un da aka kada a zaben ranar lahadi a Tunisiya

Jam’iyya mai akidar Islama mai sassaucin ra’ayi a kasar Tunisiya ta ce ta lashe kuri’un da zasu ba ta sukunin ayyana nasara a zaben da aka yi ranar lahadi, kuma ta shirya domin shata sabuwar gwamnati a wannan karamar kasa dake Afirka ta Arewa.

Wannan zabe na tarihi da ‘yan kallo suka ce an gudanar da shi ba tare da magudi ba, shi ne na farko a wata kasar larabawa inda aka fuskanci zanga-zangar da ta kawar da gwamnatocin kama-karya a fadin Afirka ta Arewa da gabas ta Tsakiya.

Koda yake sai a yau talata za a bayyana sakamakon zaben a hukumance, sakamakon farko da aka samu ya ba jam’iyyar mai suna Ennahdha kusan kashi 40 cikin 100 na adadin kuri’un da aka jefa. Akwai wasu alkaluman dake nuna cewa yawan kuri’un da jam’iyyar zata samu zai iya kaiwa kashi 50 cikin 100 ko kuma rabin dukkan kuri’un da aka jefa.

Masu jefa kuri’ar sun zabi majalisar tsarin mulki mai wakilai 217 wadanda zasu rubuta ma kasar sabon tsarin mulki ne. Alhakin majalisar ce ta tsaida irin tsarin gwamnatin da za a kafa a kasar da kuma tabbatar da ‘yancin walwalar al’umma. Kafin ta gama wannan kuma, ita ce zata nada sabuwar gwamnatin rikon kwarya.

An ce masu jefa kuri’a sun fito da yawan gaske. Hukumar zabe mai zaman kanta ta Tunisiya ta ce fiye da kashi 90 cikin 100 na mutane miliyan 4 da dubu 100 da suka yi rajista sun jefa kuri’unsu.

Tsohon shugaban kasar Peru, Alejandro Toledo, yana cikin dubban ‘yan kallo na kasashen waje da cikin gida da suka sa ido kan wannan zabe. Ya ce ba ma kawai an gudanar da wannan zabe tsakani da Allah ba ne, yadda aka tsara shi da gudanar da shi abin koyi en ga sauran kasashen duniya.

Tuni har jam’iyyar Ennahdha mai akidar Islama ta dauki matakan kafa kawancen da zai tsara gwamnati irin ta dimokuradiyya kuma wadda ba ta addini ba, ta yin koyi da irin tsarin kasar Turkiyya wadda ita ma jam’iyyar AKP dake mulkinta mai akida ce ta Musulunci.

XS
SM
MD
LG