Laraba ce hukumar kula da ‘yan gudun Hinira ta MDD ta bada labarin cewa ‘yan gudun hijira guda dari rak suka sami nasarar tsallaka kan iyakar Somaliya zuwa sansanonin ‘yan gudun Hijirar dake Kenya a makon da ya gabata. Hakan ya janyo ragin ‘yan gudun hijirar dake shiga Kenya zuwa 3,400 da aka saba gani a mako-mako.
A makon da ya gabata ne jami’an MDD suka bada rahoton cewa sojin kasar Kenya sun tsallaka kan iyaka domin farautar mayakan ‘yan tsagerar kasar Somaliya dake shiga Kenya suna boyewa. Sune kuma ke yawaita yawaiata satar mutanen da ake yi a yankin iyaka. MDD tace jibge sojin na Kenya a kan iyakokin kasashen biyu ya janyo zaman dar-dar a yankin, kuma hakan na janyo cikas ga ayyukan jin kan da jami’an MDD keyi a sansanonin kan iyakar Kenya. MDD tace akalla akwai ‘yan gudun Hijirar Somaliya miliya uku da dubu dari bakwai dake bukatar agajin gaggawa na abinchi da magunguna domin kaucewa tsanannin yunwar da ake fama da ita a yankin.