Shugaba Paul Biya Ya Koma Kamaru

Shugaban Kamaru Paul Biya

Da misalin karfe 5:30 na yamma ne jirgin da ke dauke da  Biya da iyalinsa ya sauka a babban filin jirgin saman Nsimalen.

A ranar Litinin 21 ga Oktoba Shugaban Kamaru Paul Biya ya dawo birnin Yaoundé bayan watanni bakwai da barin kasar, inda jama’a suka shiga cikin rudani ko yana raye ko yana lafiya.

Da misalin karfe 5:30 na yamma ne jirgin da ke dauke da Biya da iyalinsa ya sauka a babban filin jirgin saman Nsimalen.

Magatakardan Fadarsa, Ferdinand Ngoh da sauran jami’an gwamnati da manyan 'yan majalisa ne suka tare sBiya da iyalansa.

Magoya bayan Paul Biya, karkashin jam’iya mai mulki RDPC sun taru kwansu da kwarkwatar su a fadin titunan birnin Yaounde domin nuna murnar dawowar shugaban kasar, wanda a makonin da suka gabata aka rika yada rade-radin mutuwar shi a wasu kafafen yada labaru da wajen kasar.

Shugaba Biya mai Shekaru 92 a duniya, ya kasance akan karagar mulkin kasar ta Kamaru tun kimanin shekaru 42.

Kuma bai debe tsammanin tsayawa takarar shugaban kasa ba a zaben shekara mai zuwa.

A saurari cikakken rahoton a sauti tare da Mohammed Ladan:

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Paul Biya Ya Koma Kamaru