Shugaban Amurka Barack Obama ya bugawa takwaransa na Najeriya Goodluck Jonathan waya domin tayashi murnar nasarar zabe, yayinda yake Allah wadai da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar. A wata sanarwar da aka fitar jiya Laraba, Mr. Obama ya yabawa ‘yan Najeriya domin karfin halinsu da kuma hakuri lokutan zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisa da kuma gwamnoni da aka gudanar watan jiya. Bisa ga cewarshi, nasarar zaben shaida ce ga ‘yan Najeriya wadanda suka kuduri aniyar ganin zaben ya shata wani sabon babi a tarihin kasar. Shugaba Obama yace, yayinda akasarin ‘yan Najeriya suka kada kuri’unsu ba tare da tsangwama ba, tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 16 ga watan Aprilu bai dace da al’ummar dake bin tsarin damokaradiya ba. Tarzoma ta barke bayanda shugaba Jonathan daga kudancin Najeriya ya kada babban abokin hamayyarsa Mohammadu Buhari daga arewacin kasar. Wata kungiyar kare hakin bil’adama tace a kalla mutane 500 aka kashe a tashin hankalin.
Shugaban Amurka Barack Obama ya bugawa takwaransa na Najeriya Goodluck Jonathan waya domin tayashi murnar nasarar zabe, yayinda yake Allah wadai da tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar