Shugaban kasar Parisa/Iran Mahmoud Ahmadinejad ya la’anci duk wani matakin tura sojin kasar waje da makamai zuwa kasar Bahrain da yanzu ke fuskantar rikicin neman sauyin salon mulkin kasa.
Shugaban na kasar Iran yau laraba yake cewa kasancewar sojin larabawa daga kasashen yankin Gulf zuwa kasar Bahrain ya sabawa diyauci da dokokin kasa dakasa.
A Soja da ‘yan sanda masu tarin yawa daga kasashen Saudi Arebiya da Daular larabawa sun shiga Bahrain a makon nan domin taimakawa mulukiyar Bahrain kawo karshen zanga-zangar neman sauyin da ‘yan Shi’a masu rinjaye je yiwa salon mulkin sarautar Bahrain ta ‘yan ahalil Sunni.
Friministan kasar Birtaniya David Cameron yau laraba yayi kira ga Sarki Hamad bin Isaal-Khalifa na Bahrain da ya kokarta tafiya sannu a hankali wajen daukan matakan kawo karshen zanga-zangar ba tare da karfafa tashin hankali ba a tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar.