Harkokin tsaro a Najeriya da rike gwamnati cikin adalci su ne zasu zama kan gaba a taron kolin da shugabannin Afirka da gwamnatin Amurka keyi a birnin Washington D.C.
Kasashen waje da yawa sun fi 'yan Najeriya sanin yanayin da kasar ke ciki kuma sun san kokarin da shugaban Najeriya keyi akan harkokin tsaro. Shugaban zai yi godiya kana ya nemi karin taimako domin a shawo kan tashin tashinar da ta addabi kasar.
Dangane da ribar da Najeriya zata samu daga wannan taron Mataimakin Jakadan Najeriya Alhaji Habibu Habu cewa yayi Najeriya ita ce abun kallo. Najeriya ita ce daya kwal abun kallo a wurin taron. Ribar kuma ita ce duk wanda zai kai kudinsa Afirka ya saka jari Najeriya yake fara dubawa. Sai dai idan wani dalili ya hanashi kana ya nufi wata kasar. Duk da wai an tara shugabannin Afirka ne amma Shugaba Jonathan na kan gaba, kuma Najeriya na kan gaba.
Akan ilimi gwamnatin Najeriya ta san 'yan Najeriya sun mamaye jami'o'in kasar Ghana amma sabili da haka Shugaba Jonathan ya kara da cewa gwamnatinsa ta kara kafa jami'o'i goma sha daya tun daga lokacin da ya hau milki. Dama yayi alkawarin cewa kowace jiha zata samu jami'ar gwamnatin tarayya daya. Yanzu kowace jiha tana da jami'ar gwamnatin tarayya. Bayan su an yi wasu biyu na musamman wa 'yansanda da mayakan ruwa.
Shirin da a keyi shi ne su jihohi su inganta ilimin firamare da na sakandare sai ilimi ya kankama sosai a kasar. Yin hakan zai hana mutane zuwa waje neman ilimi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5