'Yan Najeriya mazauna Amurka suna da damuwa da yawa kuma sun bayyanawa shugaban kasa wasu daga cikinsu.
Inji Jakada Habibu Habu rashin ba 'yan Najeriya izinin yin zabe daga nan lokacin zaben gida yana cikin abubuwan da suka damesu. Duk dan Najeriya dake wajen Najeriya yana son a bashi hakinsa, wato a bari ya jefa kuri'a lokacin zabe. Alhaji Habibu yace ya kamata a basu izinin yin zabe. Yayi misali da kasar Niger. Duk inda kasar ke da ofishin jakadanci to dan kasar yana yin zabe.
Da ya koma akan rigingimun da kasar ke fama dasu sai Alhaji Habibu Habu yace duk suna faruwa ne domin mutanen kasar basu san ko su wanene ba, wato basu san juna ba yadda ya kamata. Mai Unguwa yanzu baya sanin adadin mutanen dake unguwarsa. Yayi misali da tashi unguwar Sharfadi a Kano. Mai unguwarsa ba zai iya fada yawan mutane daga masu shekaru goma sha takwas zuwa sama ba. Amma kafin 1979 idan ya bincika yana da adadin jama'arsa a rubuce. Soke haraji da jangali wadannan abubuwa biyu sun jawowa Najeriya babbar asara.
Da aka soke haraji aka dena sanin mutane. Soke jangali daga 1979 ya sa duk Fulanin da aka haifa daga lokacin yanzu basu da jiha. Yawo kawai su keyi. Amma a da duk shekara idan sun fita kiwo zasu dawo gida, za'a yiwa shanunsu huji, za'a basu magungunan da zasu ishesu har na shekara daya ba tare da biyan ko kwabo ba.
Lamarin tabarbarewar tsaro yana da alaka da kwacewa sarakunan gargajiya ayyukansu na da na rike doka da kula da tsaro. Yayi misali da jihar Jigawa inda suke zaman lafiya. Yace da gwamna Sule Lamido ya hau milki sai ya gane cewa abun da yakamata a yi shi ne a koma kan sarakuna, a bar masu jama'arsu. Sai ya je wurin sarakuna ya fada masu cewa shi gwamna da sauran mutanen duk "'yayanku ne to ku kula da mu". Sabili da haka Jigawa bata da matsalar tsaro domin an san kowa domin sarakuna an barsu sun san 'yan kasarsu. Kowane sarki ya san dan kasarsa.
Ga karin bayani.