Yawan mutanen da suka mutu a sanadin annobar cutar Ebola da ta bulla a Afirka ta Yamma ya karu zuwa kusan 900, inda aka samu rahoton sabbin mace-mace a kasashen Guinea, Liberiya da kuma Saliyo.
Hukumar kiwon Lafiya ta Duniya ta bayarda sabon adadin a yau litinin, a yayin da hukumomi a Najeriya suke bayarda rahoton cewa an samu mutum na biyu da ya kamu da wannan cuta ta Ebola a kasar. Sabon kamuwar dai, likita ne wanda yayi jinyar mutum na farko da yaje shi kasar da wannan cuta, ya kuma mutu a wani asibitin Lagos ranar 25 ga watan Yuli.
Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ce mutane dubu daya da dari shida da uku ne aka tabbatar sun kamu da wannan cuta a kasashe 4 a Afirka ta Yamma, kuma daga cikinsu, fiye da rabi, watau mutane 887, sun mutu.
A halin da ake ciki, wani likitan Amurka da ya kamu da Ebola a lokacin da yake jinyar wadanda suka kamu da cutar a Liberiya, ya fara murmurewa a asibitin Jami'ar Emory dake birnin Atlanta a nan Amurka.