Jagoran bitar Sahabo Imam Aliyu ya bayyana makasudin taron da 'yan jarida da wasu kafofin yada labarai a birnin Sokoto.
Yace dalilin bitar shi ne a roki masu yada labarai su taimaka wajen kara fadakar da jama'a mahimmancin neman ilimi. Kada a bar jahilci da wasu dalilai da basu taka kara sun karya ba a bata harkar ilimi. Kodayake akwai matsaloli da yawa dake fuskantar ilimi amma kada a bari su hana wadanda suke neman ilimin su samu.
Ana kukan talauci, ana kukan koma baya, duk wadannan abubuwa ba za'a iya kawar da su ba sai an yaki jahilci, sai an nemi ilimi. Sabili da haka Muryar Amurka da USAID suka ga yakamata su zo inda matsalar take su yi bitar, su zo kusa da jama'a, jama'a kuma su gansu. Yace yau idan kana son ka samu mutum sai ta kafofin yada labarai. Dalili ke nan suka ga yakamata su zauna da 'yanuwa 'yan jarida su sake nanatawa juna abubuwan da dama suka riga suka sani.
Sahabo Imam ya bayyana dalilin da ya sa Muryar Amurka ta zabi yin bitar a jihohin arewa. A harakar ilimi jihohin arewa su ne suke baya-baya. Yace ana kukan babu aikin yi. Kana kuma akwai wani jahilci inda aka dauka duk wanda yayi imili dole a bashi aikin yi. A'a a yi karatun domin shi ne zai kaiga samun abun yi. Amma idan an shigeshi da wata muguwar manufa to za'a samu wahala.
Wasu da suka halarci taron sun ce babu shakka taron nada mahimmanci musamman idan aka yi la'akari da yadda alamura ke tafiya yanzu. Taron shi ne na farko da Muryar Amurka ta shirya da wasu suka halarta. Sun yadda cewa matsalar ilimi a arewa babba ce.
Bitar ta horas da 'yan jarida mahimmancin karatun zamani da yadda zasu bi su inganta ayyukansu.
Ga karin bayani.