Shugaba Goodluck Jonathan yayi gargadin ne a birnin Osogbo fadar gwamnatin jihar Osun yayin da yake mikawa Sanata Omisore tutar takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP
Shugaban yana tare da mataimakinsa Alhaji Namadi Sambo da shugaban jam'iyyar Alhaji Adamu Mu'azu da shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar Tony Anenih da sauransu. Tun farko sai da shugaban ya kai ziyara ga sarakunan Ile-Ife da na Osogbo. Shugaban ya cigaba da cewa zasu tabbatar da cewa a jibge jami'an tsaro a jihar kana zasu hukunta duk wanda ya sabawa doka.
Masana harkokin siyasa suna ganin kalamun na shugaban tamkar taunar tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro ga duk wanda yake tunanin kawo yamutsi ko tada zaune tsaye lokacin zaben gwamnan jihar.
Ana zaton za'a jibge jami'an tsaro kamar yadda aka yi a jihar Ekiti. Shugaba Jonathan yace abun da suke bukata daga wurin jama'a shi ne su kadawa Sanata Omisore kuri'unsu ranar zaben a matsayin gwamnansu.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.
Your browser doesn’t support HTML5