Karamar hukumar Obi na cikin daya daga cikin kananan hukumomin da suke neman tsige 'yan majalisunsu.
A karamar hukumar Obi 'yan jam'iyyar APC na neman dan majalisa mai wakiltar yankunan Adudu, Obi, Tudun Adabu, Agwatashi da Dedere, Muhammed Sidi Bako kan ya dawo gida domin su ma su tsigeshi. Alhaji Abdullahi Anawo tsohon shugaban jam'iyyar CPC a yankin Dedere yace su suka zabi dan majalisar kuma yana yin abun da basu aikeshi yayi ba.
Kamata yayi dan majalisar ya nemi shawarar da majalisa ta tsayar daga wurinsu kana su bashi tasu shawarar abun da zai yi a madadinsu a majalisar. Ba zai yi gaban kansa ba yace zai tsige gwamna abun da basu aikeshi yayi ba. Idan ya dawo gida zasu tsigeshi.
To amma da yake dan majalisar Muhammed Sidi Bako yana jam'iyyar PDP ne 'yan jam'iyyar APC basu da hurumin cewa zasu dawo da shi domin su tsigeshi, inji jam'iyyar PDP.
Ali Idris Adudu shugaban PDP a yankin yace zanga-zangar da wasu 'yan jam'iyyar APC suka yi a mazabar Sidi Bako sun yi kuskure domin basu ne suka zabeshi ba. Su 'yan PDP suka zabeshi kimanin shekara bakwai ke nan kuma suna jin dadin aikin da ya keyi, ya kuma cigaba da aikin.
Ga karin bayani.