Kungiyar ta fara gudanar da bita akan yadda ake tattara sakamakon zabe a wannan zamanin da ake ciki.
Dr Bashir Musa Usman wanda yake zaune a Amurka yana daya daga cikin wadanda suka gudanar da bita akan yadda za'a gudanar da tsarin. Yace abun da suke son su yi shi ne a samu yadda mutane zasu samu sakamakon zabe ba na mazabarsu ba kawai a'a na duk Najeriya gaba daya. Idan aka yi zabe aka idar mutane su dakata a mazabarsu sanan ta yin anfani da naurorin salula dinsu ko abun daukan hoto idan an manna sakamakon zabe su dauki hotonsa.
Daga cikin mutanen za'a ba wasu dama su aika da sakamakon zaben ta hanyar yanar gizo ko kuma ta yin anfani da yawar salula. Duk wanda yake da burin taimakawa yana iya duba shafin kungiyar a yanar gizo wato www.voiceofvotes.com. A nan mutum zai ga bayanin yadda za'a yi.
Dr Ahmed Abubakar Gumi na cikin wadanda suka assasa kungiyar kuma ya halarci taron bitar. Yace ba wai suna son su shiga takara ba ne amma duk mai wa'azin addini uba yake ga al'umma dole ne kuma ya tabbatar an yi adalci. Ba daidai ba ne su tsaya su rungumi hannu a lokacin da ake kashe mutane ana zalunci. Dole ne su tsaya su ga an yi adalci. Dalili ke nan suka fito da tsarin da kowa zai yadda dashi.
Shi ma Bishop S. T. Usman cewa yayi taron zai taimaka wajen dora Najeriya akan hanya. Yace ya bada gaskiya idan za'a yi adalci taron zai taimaka.
To saidai Injiniya Buba Galadima yace akwai wani hanzari ba gudu ba da wannan kokarin. Yace to ba sai an ga akwatin zaben ba kuma sai an jefa kuri'ar. Idan kai baka jefa kuri'a ba to menene zaka tantance. Idan wani kato ko soja ya zo da bindiga ya harbi mutane kana ya zari akwatin zabe abun da ya ga dama zai cusa cikin akwatin. Mafita daya ce. Kowa ya tsaya tsayin daka cewa mutane sun jefa kuri'u kuma an kirgasu.
Ga karin bayani.