ZABEN2015: Shugaba Jonathan Ya Ce Ba Za'a Yi Yaki Akan Zabe Ba

Shugaba Jonathan na tattaunawa da 'yan jarida.

Shugaban na kasar Najeriya yayi wannan furuci ne da yammacin Laraba a lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida kan batutuwa daban-daban.

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya baiwa 'yan Najeriya tabbacin cewa babu wanda zai yi yaki saboda zaben shekarar dubu biyu da goma sha biyar.

Shugaban ya furta hakan ne da yake amsa tambayoyin da 'yan jarida su ka yi ma sa game da irin maganganun tsokanar fadan da 'yan uwan sa na yankin Niger Delta suke yi gami da barazanar cewa za su raba kasar Najeriya idan ba shi ya ci zabe ba.

Haka kuma shugaban na kasar Najeriya ya musanta jita-jitar da ake ta bazawa cewa wai, zai sallami Farfesa Attahiru Jega daga matsayin sa na shugaban hukumar zabe, sannan kuma ya kara jaddada cewa yawancin tallace-tallacen yakin neman zaben da ake yi ma sa, ana yi ne ba da yawun sa ba, ya ce ba shi da masaniya a kai.

Shugaban ya zanta ne da 'yan jarida akan wasu muhimman batutuwan da suka shafi maganar zaben Najeriya.

A wata gab'a ta daban, shi ma tsohon shugaban mulkin soja na kasar Najeriya Abubakar Abdulsalami yayi kira a kwantar da hankali kuma yayi kira ga ma'aikatan zabe su yi gaskiya. Hakazalika sakataren amintattun jam'iyar PDP, Walid Jibril yayi kira ga 'yan Najeriya su kai zukata nesa, ya ce bai laifin hukumar zabe ba ne kuma ba laifin Attahiru Jega ba ne, amma kafin nan shi ma dan takarar shugaban kasar jam'iyar APC, janar Muhammadu Buhari ya kara jaddada dalilan da suka sa aka dage zabe sannan yi kira ga magoya bayan sa su maida wuka kube.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaba Jonathan ya ce babu wanda zai yi yaki akan zabe - 2'22"