Farfasa Attahiru Jega shugaban hukumar zabe ko INEC a takaice yace idan dalilin ajiye aikin ya zo zai ajiye.
Farfasa Jega yana mayarda martani ne ga masu kiran yayi murabus wadanda suka hada da dattijon yankin Niger Delta da shugaba Jonathan ke girmamawa, Chief Edwin Clark.
Raderadi sun fito a jaridu dake cewa akwai wani shirin kawar da shugaban hukumar zaben Farfasa Attahiru Jega. Sai kuma a nada wanda zai zama dan amshin shata.
Sai dai tuni wasu sun shiga babban kotun tarayya domin kalubalantar Janaral Buhari akan dambarwar takardar kammala ilimin sakandare.
'Yan kungiyoyin fararen hula da wasu 'yan jam'iyyun adawa na matsa lamba a bi ranar da aka tsayar domin sake dageta ka iya kawo rudanin tasrin mulki.
Alhaji Abubakar Abdullahi Sokoto sakataren jam'iyyar UPN yace tabarbarewar tsaro ba hujja ba ne na dage zaben. 'Yan Najeriya sun dawo daga rakiyar hukumomin tsaron Najeriya saboda abubuwa guda uku. Sun yi karya akan 'yan matan Chibok. Sun fada suna shiri da kungiyar Boko Haram amma abun ya zama holoko hadarin kaka.Sun ce sun kashe Abubakar Shekau shugaban Boko Haram abun ya zama karya. Babu wata maganar da zasu fada da 'yan Najeriya zasu yadda da ita.
Dan adawa Sa'ad Abdullahi na nuna damuwa da abun da ya gani yadda jami'an tsaro ke tsoma baki akan harkokin zaben. Yadda hukumomin tsaro ke gudanar da aikinsu zai kai kasar ga halaka.
Jam'iyyar PDP dai tace bata shirya wata kumbiya-kumbiya akan zaben ba. Su ma jam'iyyu dake da kawance da PDP sun ce dage zaben bashi da wani lahani ga dimokradiya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.