Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Rikici Ya Barke a PDP Reshen Borno


Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon gwamnan jihar Borno
Sanata Ali Modu Sheriff, tsohon gwamnan jihar Borno

Takaddama ta taso akan wanda zai tsaya takarar sanata karkashin PDP din a Borno ta tsakiya.

Tsoffn 'yan PDP na ainihi tun kafin tsohon gwamnan jihar Ali Modu Sheriff ya canza daga APD zuwa PDP suna da nasu dan takara.

Yanzu da tsohon gwamnan ya shiga PDP ya ayyana kansa a matsayin dan takarar jam'iyya yana kuma ikirarin cewa uwar jam'iyya ta kasa ta bashi takarar kujerar. To sai dai tsohon bangaren ya gabatar da Kanal Mohammad Baba Kachalla.

Bayan bangarorin biyu sun dan jima suna kai ruwa rana sai gashi Kanal Mohammad Baba Kachalla ya fito fili ya shaidawa jama'a cewa shi ne hukumar zabe ta sani a matsayin dan takarar PDP na Borno ta tsakiya.

Tun shigar Sanata Ali Modu sheriff PDP wasu magoya bayansa suka dinga cewa shi tsohn gwamnan ne zai tsaya masu takara a Borno ta Tsakiya. Shi din ya gayawa jama'a cewa magoya bayansa sun saya masa takardar tsayawa takara.

Daya daga cikin magoya bayan Ali Modu Sheriff ya bayyana shi, Ali suka sani domin ya farfado da PDP a jihar daga mutuwar da tayi.

Shugaban PDP na jihar Alhaji Baba Yashau ya shaidawa wakilin Muryar Amurka cewa sunan Kanal Muhammad Baba Kachalla suka bayar.

Ga rahotn Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG