A kasar Najeriya kowane laifi za'a fada ba za'a ce Murtala Nyako ne kadai yayi ba. An cire gwamnan ne domin yana APC kuma sabili da wasu dalilai da ba sai anfada ba inji gwamnan Kano.
Gwamnan ya kara da cewa tsarin da suke tafiya da shi yanzu ya zama duk wani babban azzalumi a kasar babu inda zashi ya buya sai a cikin jam'iyyar PDP. Da Murtala Nyako yana cikin PDP ne inji gwamnan Kano ya tabbata da ba za'a cireshi ba. Yace wannan shi ne kashe dimokradiya idan kuma aka cigaba da yin hakan an kashe dimokradiya ne gaba dayanta.
Tuni masu fashin baki suka fara tofa albarkacin bakinsu dangane da tsige gwamnan na Adamawa da kuma yunkurin kawar da takwaransa Umaru Tanko Al-Makura na jihar Nasarawa. Malam Albati Bako daraktan cibiyar harkokin siyasa da dimokradiya ta kasa da kasa yace salon da siyasa ta dauka yanzu na tsige gwamna idan aka cigaba da yin hakan dimokradiya zata shiga cikin wani wusufi. A shekarar 1981 an cire gwamna Balarabe Musa na tsohuwar jihar Kaduna. A zaben 1983 NPN ta kwace jihohin 'yan hamayya. Amma daga karshe ita kanta dimokradiya ta wannan lokacin dole ta shiga cikin wusufi ,wato ta durkushe ta mutu. Shin yanzu ba tarihi ba ne zai maimaita kansa.
Tsarin mulki ya shimfida ka'idodin da za'a bi a cire duk gwamnan dake almundahana da dukiyar jama'a. Amma ya zama wajibi a bi ka'idodin daki-daki domin an yi maganar cewa akalla za'a dauki tsawon wata uku kafin a kaiga tsige gwamna to amma a Adamawa a cikin kwana biyu aka tsige gwamnan. Wannan ya nuna akwai shinshini, wato gwamnatin tarayya tana bin gwamnonin dake hamayya da ita tana tsigesu. Irin wannan lamarin shi zai jawo rugujewar dimokradiya a kasar.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5