A jihar Adamawa jam'iyyar PDP ke da rinjaye a majalisar dokokin jihar. Kuma lokacin da gwamnansu Murtala Nyako ya bar jam'iyyar zuwa APC 'yan majalisar biyar kawai suka bishi wadanda su ma daga baya sun koma PDP.
Siyasa a jihar Adamawa wani abu ne daban. Ta sha banban da sauran bangarorin Najeriya. Manyan 'yan jihar da Allah ya albarkacesu basa shiri da juna. Kowa gabansa ya kama. Sabo da haka wanda yake gaba sai ya zama abokin gaban kowa.Yace sun dade suna nazarin shin wai menene ya sa manyan Adamawa suna da wannan kalubale.
Dr Kabir Mato yayi misali da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. Lokacin da za'a kawo Murtala Nyako ya zama gwamna sai da suka yi nazari cewa babu wanda zai iya kwato Adamawa daga shiga hannun Atiku Abubakar sai an sa Murtala Nyako. PDP ta kwace jihar ta ba Murtala Nyako. To saidai dangantaka tsakaninshi da sauran sai ta baci, musamman tsakaninshi da tsohon shugaban PDP Alhaji Bamanga Tukur.
Kuskuren Gwamna Murtala Nyako shi ne gazawar da yayi wurin komawa APC tare da 'yan majalisarsa kacokan kamar yadda gwamnan Kano yayi.
Ga karin bayani.