Wata majiya mai tushe kusa da shugaba Goodluck Jonathan ta ba Sashen Hausa Muryar Amurka jawabin shugaba Goodluck Jonathan da aka nada, lokacin da ya yiwa shugaba mai jiran gado, Muhammadu Buhari waya, da ya nuna ya rungumi kaddara bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Asabar da Lahadi. Mr Jonathan ya yabawa wanda ya lashe zaben ya kuma gayyace shi, yaje su tattauna kan shirin mika mulki.
Shugaba Goodluck Jonathan ya ranar 31 ga watan Maris yana cewa
“Na gode kwarai mai girma shugaban kasa, I, yaya al’amura?”.
Idan ka sami lokaci wata rana kazo, domin mu soma shirin yadda za a mika mulki.
To mai girma shugaban kasa, na gode kwarai, yayi kyau, ina tayaka murna, na gode mai girma shugaban kasa. Ina ban girma.
Shugaba Goodluck Jonathan na jam’iyar Peoples Democratic-PDP ya sha kaye a zaben da tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari na jam’iyar All Progressive Congress-APC ya lashe,zaben da aka gudanar cikin kwanciyar hankali ranar 28 da 29 ga watan Maris shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.
Wannan ne karon farko da shugaban kasa mai ci ya fadi zabe a Najeriya.
Masu sharhi kan lamura sun ce, ba kasafai ake samun wadanda suka tsaya takara suna rungumar kaddara ba bayan sun fadi zabe a kasashen nahiyar Afrika,sai dai wadansu suna yi.
Shugaban kasa mai jiran gado, Janar Buhari zai karbi mulkinkasar da tafi kowacce yawan al’umma da karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, ranar 29 ga watan Mayu.
Tattalin arzikin Najeriya yana fuskantar koma baya, sabili da faduwar farashin mai da kuma tada kayar baya da kungiyar Boko Haram take yi a arewa maso gabashin kasar. Kungiyar mai tsatsauran kishin Islama tana garkuwa da sama da yammata 200 daliban makarantar sakandaren da ta sace a garin Chibok dake arewa maso gabashin kasar a cikin watan Afrilun bara. Kimanin ‘yammata hamsin sun bukuta da kansu, sai dai har yanzu ba a gano galibinsu ba.